KALLABI: Tattauna Akan Tasirin Takarar Kamala Harris Ga Mata Duk Da Yake Bata Samu Nasara Ba, Nuwamba 10, 2024

Alheri Grace Abdu

A ranar talatar data gabata Amurkawa suka nufi rumfunan zabe inda suka sake zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasa karo na biyu, bayan ya sha kaye shekaru hudu da suka gabata.

Yayinda Takarar mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat a zaben 2024 ya ci gaba da daukar hankalin Mata a kasashen duniya duk da yake bata samu Nasara ba, amma takarar tata ta baiwa Mata kwarin gwiwar fafutukar neman a dama da su, da zaburar da mata a nahiyar Afrika wandanda suka dade suna neman a dama da su a harkokin siyasa. Shirin kallabi zai tattauna akan tasirin takarar Kamala Harris.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KALLABI: Tattauna Akan Tasirin Takarar Kamala Harris Ga Mata Duk Da Yake Bata Samu Nasara Ba, Nuwamba 10, 2024