A karshen makon da ya gabata ne aka samu labarin bullar sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a shiyar Sakkwato, duk da yake sun dade suna gudanar da ayyukan su a wasu kananan hukumomi na jihar.
Bayanan da Sahen Hausa ya tattara daga mutanen yankunan Tangaza da Binji sun nuna cewa, wadannan mutanen sukan zo dauke da manyan makamai suna baiwa mutane umurni a kan abinda ya shafi addinin musulunci, kamar zakka da sallah da makamantan haka.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin yankin da suke shigowa ta Tangaza, wanda ya saba da ayyukan su a kasar Mali da yake yana tafiye tafiye zuwa Mali, wanda ya bukaci a sakaya sunansa bisa dalilan tsaro ya bayyana yadda wadannan mutane ke ayyukan a kasar Mali da kuma a nan yankunan da suke shigowa a Najeriya.
Ko a makon jiya da mahalarta kos na 33 na kwalejin horas da dubarun tsaro ta Najeriya suka je Sakkwato domin ziyarar aiki, dangane da kwas din da suke sai da mataimakin gwamnan Sakkwato ya yi musu bayani a kan wannan kungiyar.
Yace an san kungiyar a zaman ta 'yan kishin addini, kuma binciken da aka yi ya nuna suna dauke da muggan mukamai, sai dai kuma duk haka jami'an tsaro na aiki babu kyakkyaftawa don magance barazanar da wadannan mutanen suka haifar, yace gwamnati aiki kut da kut da jami'an tsaro na gwamnatin tarayya domin maganin wannan matsalar.
To sai dai masana -tsaro na ganin akwai bukatar gwamnati kada ta dauki wannan batun da sassauci, kamar yadda masanin tsaro Detective Auwal Bala Durumin Iya ke cewa.
Mutanen yankin sun bayyana cewa duk da yake ba su cutar da kowa, hasali ma suna fada da barayin daji dake haddabar mutanen yankukan, akwai shakku da fargaba kan abinda zasu iya zama nan gaba, musamman duba da cewa suna dauke da manyan makamai.
Tuni dai bayanai a manyan jaridun kasar suka nuna cewa, Rundunar tsaron Najeriya ta bakin daraktan hulda da kafafen yada labarai na ayyukan tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da bullar wadannan mutane da ke ayyukan su a yankunan jihohin Sakkwato da Kebbi.
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5