A DAWO LAFIYA: Tattaunawa Da Mataimakin Shugaban Kungiyar NARTO shiyar Arewa Maso Yammacin Najeriya

Baba Makeri

Shirin na wannan makon ya kawo muku ci gaba da tattaunawa da wakilin Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari da Alhaji Sani Idi Danfulani, mataimakin shugaban kungiyar masu motoci ta kasa ta NARTO shiyar Arewa maso yamma a kan batun diban mai a lokacin da motar dakon man fetur ya yi hatsari, lamarin da kan tada gobara har ya kai sanadiyar mutuwar daruruwan mutane kamar yanda ya faru a makwanni uku da suka shude a garin Majiya na karamar hukumar Taura a jihar ta Jigawa, ga dai ci gaban tattaunawar.

A saurari shirin tare da Baba Yakubu Makeri:

Your browser doesn’t support HTML5

A DAWO LAFIYA 11-02-24.mp3