Washington, DC —
Shirin na wannan makon ya kunshi ci gaban tattaunawar da wakilin mu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya yi da Alhaji Sani Idi Danfulani mataimakin shugaban kungiyar masu motoci ta kasa ta NARTO shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya a game da dabi’ar zuwa kwasan man fetur a sa'adda aka samu hatsarin manyan motocin dakon, lamarin da ke sanadiyar asarar rayuka a lokaci guda, kamar yanda ya faru a makon jiya a garin majiya da ke karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.shirin ya kuma tabo batun wani hatsarin jiragin sama mai saukar ungulu da ya auku a ranar Alhamis, wanda ya yi sandiyyar mutuwar mutane biyar a birnin Fatakwal, fadar gwamnatin jihar Ribas.
A saurari sautin shirin tare da Baba Yakubu Makeri:
Your browser doesn’t support HTML5