Shirin na wannan makon ya duba wani babban al’amarin dake sanadiyar asarar rayuka masu dimbin yawa a kasashe masu tasowa musamman ma a tarayyar Najeriya mai arzikin man fetur, inda mutanen gari kan yi yunkurin diban mai a sa'adda manyan motocin dakon mai suka yi hatsari.
Masu ruwa da tsaki su kan tsawata wa al’umma da su kaucewa wannan dabi’a amma kuma babu wani takamaiman matakin kariya da ake dauka.
A farkon wannan mako an yi asarar dimbin rayuka a jihar Jigawa, inda Gwaman Jihar Umar Namadi ya jagoranci taron jana'izar mutane fiye da dari da suka rasa rayukansu a sanadiyyar gobarar da ta tashi bayan da wata motar dakon man fetur ta fadi a garin Majiya kake karamar hukumar Taura a jihar ta Jigawa.
A wani bangaren kuma, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar tace alkaluman wadanda suka mutu suna dada karuwa.
Inda ta ce bayan kwanaki biyu da faduwar tankar dakon man fetur na garin Majiya a jihar Jigawa ya tasamma 170 yayin da sama da mutane 60 ke ci gaba da karbar magani a asibitoci daban daban.
Al’ummar kauyen da lamarin ya faru sun bayyana cewa, sun koyi darrusa da yawa.
Wakilin muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya tattauna da Alhaji Sani Idi Danfulani, mataimakin shugaban kungiyar masu motoci ta kasa NARTO shiyyar Arewa maso yamma a kan batun.
A suarari sautin shirin tare da Baba Y. Makeri:
Your browser doesn’t support HTML5