Gwamnatin Isra’ila ta ce Lebanon ta auna gidan firan ministan kasar da jirgi marasa matuki yau asabar, ba tare da wani ya rutsa da wanii ba, yayin da shugaban addinin Iran ya sha alwashin cewa Hamas zata ci gaba dayakin ta da Isra’ila bayan da ta kashe mutumin da ya kitsa mummunan harin da Hamaz ta kai Isra'ila bara a ranar 7 ga watan Oktoba.
Gwamnatin Isra’ila ta ce tashiwar kararrawa da safiyar ranar asabar a Isra’ila, ya fargar da su harin jirgi marasa matuki daga Lebanon, wanda aka auna gidan Firan Minista Benyamin Netanyahu a Caesarea.
Firan ministan da uwar gidar sa duk basa gidan a lokacin da aka kai harin, sannan babu wanda ya jikkata, a cewar mai magana da yawun firan ministan cikin wata sanarwa.
A watan Satumba, mayakan Houthi sun harba makaman mizal da ya auna filin jiragen saman Gurion a sa’adda jirgin da Netanyahu yake ciki yake harramar sauka.
Harin da aka kai cikin Isra’ila na ranar asabar na zuwa ne a sa’adda ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Hezbollah a Lebanon, wata kawar Hamas da ke samun goyon bayan Iran, wanda ya dada zafafa cikin ‘yan makonnin da suka gabata. Amurka, Birtaniyya da tarayyar Turai da sauran kasashen yamma, sun ayyana Hamas da Hezbollah a matsayin kungiyoyin ta’addanci.
Hezbollah ta fada ranar Jumma’a cewa tana shirin bude wani sabon shafi a fadar da takeyi ta yadda zata harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka masu fashewa cikin Isra’ila. An kashe Hassan Nasrallah wanda da ya dade a matsayin shugaban kungiyar mayakan, a wani harin saman da Isra’ila ta kai a karshen watan Satumba, sannan Isra’ilar ta aike dakaru cikin Lebanon ta kafa a farkon watan Oktoba.
Bayan da harin jirgi marasa matakin da aka auna gidan Netanyahu da si, Sojojin Isra’ila sun ce an harbor wasu jirage marasa matukan 55 daga Lebanon, a wasu hare haren a arewacin Isra’ila da safiyar yau asabar. An kakkabo wasu daga cikin su acewar sojojin, sannan babu wani rahoto kan wadanda suka yi rauni.