Ukraine Da Rasha Sunyi Ikirarin Dakile Hare Haren Jirage Marasa Matuka Da Dama

Russia Ukraine War

Rasha ta fada ranar asabar cewa, ta dakile hare haren jirage marasa matuka 47 da Ukraine tayi yunkurin kai mata hari da su, yayin da Kyiv itama ta bada rahoton kakkabo jirage marasa matuka 24 da Moscow ta yi yunkurin kai mata hari da su. Sojojin saman Ukraine sun ce an harbo makaman missile da dama daga yankin Belgorod na yankin kan iyakar Rasha, ba tare da wani bayyana akan irin makaman nukiliyan ko adadin su ba.

Ta ce Rasha ta auna Ukraine da jirage marasa matuka 28, wanda ta kakkabo 24 cikin su a yankin Sumy, Poltava, Dnipropetrovsk, Mikolayev da Kherson.

Kazalika, shugaban ma’aikatan Ukraine ya ce dakarun Kyiv sun yi nasarar auna wani ma’ajin mai cikin dare a gabashin yankin da Rasha ta mamaye a Lugansk, lamarin da ya haddasa gobara. Bata bata yi wani karin bayani ba.

Moscow bata tabbatar da kai wannan harin ba. Sai dai, ma’aikatar tsaron Rasha ta ce dakarun ta sun kakkabo jirage marasa matuka 47 da Ukraine ta yi yunkurin kai mata hari da su cikin dare, wanda suka hada wurare guda 17 a kudu maso gabashin yankin Krasnodar, 16 a yankin tekun Azov da guda 12 a yankin kan iyaka dake Lursk.