Gwamnatin Barno Ta Fara Rabon Kudi Da Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zullum.

Gwanan Jihar Borna ya jagoranci fara rabon kudin tallafi ga al’ummar jihar da ibtila’in ambaliyar ruwa ta rutsa da su wanda aka tara musu a asusun tallafin da aka samar bayan ambaliyar da ta auku bayan fashewar madatsar ruwan Alu a watan da ya gabata.

Gwamna Baba Gana Umara Zulum, ya kuma kara da bayani cewa, zasu kiyasta irin barnar da ambaliyar ta yi sannan zasu tantance ainihin wadanda al’amarin ya rutsa da, kana y ace bazasu lamunci sama da mutum daya daga iyali daya su karbi kudi ba, kuma duk wanda suka sameshi da laifin yin hakan zai fuskanci fushin hukuma.

Za a baiwa wadanda al'amarin ya rutsa da su kudi daga naira dubu dari (100,000:00) zuwa naira miliyan daya (1,000,000:00), kwatankwacin irin barnar da ambaliyar ta yi. Gwamnan yace har yanzu dai suna dakon tallafi daga gwamnatin tarayyar Najeriya.

A saurari rahoton Ibrahim Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Update On Borno Floods.mp3