Rasha Ta Kai Harin Jirage Mara Matuka Da Makamai Masu Linzami Ukraine Cikin Dare

Russia Ukraine

Jami'ai sun fada a ranar Lahadi cewa wani mutum guda ya mutu bayan da dakarun Rasha suka kai hari Ukraine cikin dare da jirage marasa matuka samfirin Shahed 87 da mabanbantan makamai masu linzami.

Gwamnan yankin Oleh Syniehubov, ya ce "an kashe wani mutum mai shekaru 49 a yankin Kharkiv, bayan da wani jirgi mara matuki ya afkawa motar sa.

An lalata wani bututun iskar gas, sannan an cinna a wani dakin ajiya a birnin Odesa, a cewar jami;an Ukraine.

AN kai wannan harin, wuni daya bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya fada a ranar asabar cewa, zai gabatar da shirin da zai kai shi ka samun nasara a wurin taron kungiyar kasahen dake baiwa Ukraine tallafin makamai Ramstein wanda za agudanar a ranar 12 ga watan Oktoba.