Taron Bunka Cinakayya Tsakanin Damagaram, Daura, Jigawa Da Kano

  • Ibrahim Garba

Hada Hadar Kasuwa

A ci gaba da sake bunkasa huldar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar, tun bayan warware rigimar da ta biyo bayan takunguman ECOWAS, kungiyar PRODAF ta inganta tsarin kasuwanci tsakain Damagaram, Daura, Jigawa da Kano, ta yi wani babban taro a Damagaram, Janhuriyar Nijar, da zummar komawa kan shirin nan na bunkasa nau’ukan noma da kasuwancin da kowannensu ya fi yin fice a kai.

Muhammad Rufa’i, Babban Jami’in saukaka kasuwanci tsakanin Nijar da Najeriya, ya yi karin bayani ma wakiliyar Sashin Hausa a Damagaram, Tamar Abari da cewa daga abin da aka cimma a wurin taron na Damagaram za a dora.

'Yan kasuwan kasashen biyu, musamman ma daga garuruwan nan hudu da su ka fai cinakayya da juna, kan koka kan tsaurin ka'odojin cinakayyar, wadanda kan gurgunta harkokin tattalin arzikinsu alhalin kuwa za su amfani juna, ganin kowannensu na da wadatar wani abu da sauran ke matukar bukata.

Sauran masu ruwa da tsaki sun yi bayani a hirarsu da wakiliyar Sashin Hausa.

Saurari rahoton Tamar Abari:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Korido.mp3