Andulus (Spain) Ta Karbi Bakuncin Taron Batun Kafa Kasar Falasdinu

  • Ibrahim Garba

Taron Batun Kafa Kasar Falasdinu

Kasashen duniya na ci gaba da fadi tashin ganin an samu mafita a rikicin Gabas Ta Tsakiya ta wajen daukar matakin da zai dan gamshi kusan kowa, kuma kowa zai hakura da abin da ya samu.

Jiya Jumma’a, a daidai lokacin da kasar Spain ke karbar bakuncin wani muhimmin taro, na nazarin batun kafa kasar Falasdinu, daruruwan masu makoki, sun halarci jana’izar wasu mutane biyar na garin Tuba da ke Yammacin Kogin Jordan, wadanda su ka mutu a wani harin jirgin sama da Isira’ila ta kai ranar Laraba.

Masu makokin sun yi tattaki a kan titunan birnin Tuba jiya Jumma’a din, dauke da gawarwakin mamatan hudu a makara. Wasunsu na kada tutocin kungiyar Hamas. Mutum na biyar da aka kashe, shi ma an binne shi jiya Jumma’a a garin Tamoun, wanda shi ma ke sashin arewa na Yammacin Kogin Jordan.

A wani bayani, rundunar sojin Isira’ila, ranar Laraba, ta ce wani jirgin yakinta ya auna wata mabuyar masu harkar ta’addanci mai kunshe da ‘yan ta’adda biyar, wadanda ke dauke da bama bamai kuma su ke barazana ga sojojin Isira’ila. Ma’aikatar Lafiyar Falasdinu da ke Yammacin Kogin Jordan, ta tabbatar da adadin mace macen, to amma ba ta yi karin bayani kan ko shin wadanda sojojin Isira’ila su ka kashe din mayaka ne ko farar hula ba.

Sojojin Isira’ila sun kaddamar da jerin matakan soji a sashin arewa na Yammacin Kogin Jordan cikin makwanni biyu da su ka gabata, inda su ka fi tsananta hare hare kan Jenin, Tuba, da Tulkarm. Duka biranen uku na dauke da bangarorin mayaka irinsu Hamas, da al-Jihad al-Islami fi Filastin, wadda Iran ke daukar nauyinta, da kuma Fatah.