Yayin da ambaliyar ruwa take ci gaba da barna a sassan Najeriya, jihohin Borno da Yobe suma basu tsira ba inda ambaliyar ruwan tayi sanadiyar mutuwar mutane takwas a jihohin biyu kamar yadda wakilin Muryar Amurka a yankin Ibrahim Mustapha ya ruwaito cewa cikinsu harda kanana yara a jihohin Borno da Yobe, adalilin ambaliya wadda yay sanadin lalata gonaki dadama, ciki harda gidaje.
Yan uwan wadanda ambaliyar ruwan tayi sanadiyyar rasa ransu a jihar Borno, sun mika faruwan lamarin ga Allah suna masu danganta faruwan lamarin a matsayin kaddara daga Allah.
A jihar Yobe kuma, ambaliyar tayi sanadin mutuwar yara kanana su uku wadanda suka fita wasa ambaliyar ta cinye su a garin Nguru, dake yankin arewa maso yammacin jihar Yobe.
Ambaliyar ruwan ta lalata hanyoyi da dama da suka hade jihar wasu sassan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya. Ambaliyar ta kuma lalata gonaki, da rusa gidaje, a garuruwan da suka hada da Jumban, Nangere, Jakusko, Bursari Gashua Bade duk a jihar Yoben.
A jihar Borno kuma, ambaliyar ta shafi yankunan Damasak da Chibok, inda kogin Gadabul dake kewaye da sassan jihohin Arewa maso gabashi ya dayo wadda yake hade da yankin tafkin chadi.
A jihar Borno kuma, ambaliyar ta yi barna a kananan hukumomi da dama sannan ta lalata gonaki da yanzu an wakilta wata tawaga ta musamman da aka dorawa alhakin bibiyar al’amuran ambaliyar a jihar ta Borno.
A saurari rahoton Ibrahim Mustapha:
Your browser doesn’t support HTML5