'Yan Ikilisiyar Methodist Sun Yi Zanga-Zangar Kyamar Auren Jinsi

membobin Ikilisiyar Methodist suna zanga zangar kyama da auren jinsi a Zimbabwe

Mabiya Addinin Kirista Iklisiyyar United Methodist Church a Najeriya, sun gudanar da zanga zanga ta lumana don nuna kyama ga batun auren jinsi da wassu Shugabannin Iklisiyar Methodist Church ke kokarin ganin mabiyan sun amince dashi.

An gudanar da zanga zangar ne a Hedkwatar Iklisiyar Methodist Church da ke garin Gwamdun a karamar Shongom ta jihar Gombe.

Mabiyan sun gudanar da zanga zangar ce tare da rike kwalaye mai dauke da rubutu dake Allah Wadai da batun auren jinsi,madigo da kuma Luwadi.

Daga bisani, bakon da majalisar Bishop bishop na kasar Amurka ta turo, Bishop John Schol, yace ya zo ne domin daidaita al’amurra ba batun auren jinsi da kuma Luwadi ba, domin ya san cewa, Najeriya bata yarda da aikata Luwadi ba.

malaman-addini-a-malawi-sun-yi-zanga-zangar-nuna-rashin-amincewa-da-auren-jinsi-daya

nijer-ta-kama-hanyar-soma-hukunta-yan-luwadi-da-masu-madigo

Darektan Ma’aikatan Methodist Church shiyyar Jihohin Arewa, Filiyobas Audu ya yi Karin haske dangane da manufar zanga-zangar tare da bayyana cewa, Littafi Mai Tsarki bai yarda da auren jinki ko luwadi ba.

Saurari cikekken rahoton Abdulwahab Mohammed:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Ikilisiyar Methodist Sun Yi Zanga-Zangar Kyamar Auren Jinsi