DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Hanyoyin Magance Shan Miyagun Kwayoyi A Arewacin Najeriya-Kashi Na Uku, Yuli 11, 2024

Alheri Grace Abdu

Idan kuna biye shirin Domin Iyali, makonni biyu da su ka shige, shirin ya karbi bakuncin Dr Zarah Yusuf shugabar wata kungiya da ke kula da mata da kananan yara a Damaturu, jihar Yobe, da hajiya Aisha Mohammed Yakasai, shugabar kungiyar mata mai tarbiya a jihar Kano, da kuma magidanci alhaji Abdullahi Umar Kwarbai domin nazarin batun karuwar shan miyagun kwayoyi a arewacin Najeriya da ake samu tsakanin mata, har da matan aure da zaurawa.

Bakin namu sun bayyana zaman kashe wando a matsayin daya daga cikin dalilan samun mata suna shiga shan miyagun kwayoyi.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

DOMIN IYALI: Tattaunawa Kan Hanyoyin Magance Shan Miyagun Kwayoyi A Arewacin Najeriya-Kashi Na Uku