KALLABI: Ci Gaba Da Tattaunawa Da Masu Kula Da Lamura Akan Tasirin Bikin Ranar Yara Ta Najeriya - Yuni 09, 2024

Alheri Grace Abdu

Shirin Kallabi na wanan makon zai ci gaba da haska fitila akan Ranar yara a Najeriya, 27 ga watan Mayu na kowacce shekara ranar da kasar ta kebe a matsayin ranar yara da nufin karrama kananan yara daga kasa zuwa matakin sakandare.

Hukumomi a Najeriya sun shafe kusan shekaru sittin suna bikin ranar kananan yara duk shekara, sai dai kamar yadda Malaman da shirin Kallabi ya zanta da su suka bayyana, ranar bata da wani tasiri a rayuwar yaran ko kuma makomarsu a cewar Malama Hauwa Lawal Jibril da Hadiza Tata Gwani, Malaman da suka share sama da shekaru 53 tsakaninsu suna koyarwa, kuma za a iya cewa, sun ga jiya, sun ga yau a fannin ilimi.

Sannan shirin ya tattauna da Zainab Mohammed Bununu wata ‘yar fafatukar kare hakkokin mata matashiya daga jihar Bauchi, inda ta zanta akan koma baya da mata ke samu a fannin siyasa.

Saurari cikakken shirin da Grace Alheri Abdu ta gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

KALLABI: Ci Gaba Da Tattaunawa Da Masu Kula Da Lamura Akan Tasirin Bikin Ranar Yara Ta Najeriya - Yuni 09, 2024