AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: A Lahira Wa Zai Biya Bashin Da Kasa Ta Ci? Yaya Man Jirgin Sama Ya Ke Ne?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalamu a laikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na Amsoshin Tambayoyinku; da fatan masu azumi kuma ana ayyukan ibada lafiya.

Tambayoyi

Yau za a ji amsar wata tambaya mai cewa, “VOA HAUSA, kwanakin baya mun ji gwamnatin Najeriya na neman kasashen duniya su yafe mata bashin da suke bin ta. Don haka, don Allah ku tambaya mana malamai, cewa shin idan kasashen su ka ce ba su yafe ba; in mun je lahira, talakawan Najeriya ne za su biya wannan bashin ko shugaban ƙasa?.”

Masu Tambayar: Jamila, da Fati, matan Ado Salati Goma Ga Annabi Rijau, da A’ishan Usaini Ɗangote Karasuwa, da Maryam Babagana Alhaji Nuciya Wacakal, da Maimunan Aliko Auta Kafinta Yelwa.

Za kuma a ji amsar wata tambaya mai cewa: "Wai shin wani irin mai ne jirgin sama ke sha?"

Mai Tambayar: Musa Is’hak Bauchi, da Abubakar Yakuba.

Amsoshin

To, bari mu fara da amsar tambaya mai cewa tsakanin talawaka da Shugaban kasa wa zai biya bashin da kasa ta ciwo, idan ba a biya ba har aka je lahira? Shugaban Majalisar Malaman Izala Shiyyar birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Wakilin Malaman Bauchi, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, ya yi bayani.

Sai kuma amsar tambaya kan man da jirgin sama ke sha, wadda Alhaji Adamu Ahmad Arena, wani tsohon Ciyaman din kungiyar IPMAN ya amsa mana.

A sha bayani lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

03-23-24 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU - Bashi-Lahira-Jirgi.mp3