Shugaba Tinubu Ya Halarci Taron Ranar Tunawa Da Mazan Jiya

Bola Tinubu

Daga daya zuwa gomasha biyar ga Jana'irun kowace shekara, gwamnatin Najeriya, kama da ga matakin tarayya har zuwa jihohi, sukan gudanar da bukukuwa na tunawa da sojojin da suka sadaukar da rayukan su wajen ganin kasar ta tsayu da kafafunta.

Taron da ya gudana a yau Litinin a babban birnin tarayya Abuja, ya sami halartar manyan sojoji da jami'an gwamnati na kasa.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Daga daya zuwa gomasha biyar ga Jana'irun kowace shekara, gwamnatin Najeriya, kama da ga matakin tarayya har zuwa jihohi, sukan gudanar da bukukuwa na tunawa da sojojin da suka sadaukar da rayukan su wajen ganin kasar ta tsayu da kafafunta.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

A lokutan bukukuwa akan tara kudi ga iyalan 'yan mazan jiya, da gudanar da addu'o'i da bukin girmamawa ga wadanda suka rasu a fagen daga, inda muhukunta ke tsokaci akan gudunmuwar da sojojin suka bayar.

Da ga dama Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, Ministan Abuja, Nyesom Wike da Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

To sai dai wasu daga cikin 'yan mazan jiyan na ganin abinda suka yi wa Najeriya ya kamata ace ana basu kulawa fiye da bukukuwan shakara-shekara.

Shugabanin jami'an tsaron Kasar Najeriya.

Mahukunta sun yi amannan da cewa 'yan mazan jiyan sun bautawa Najeriya yadda ya kamata, kamar yadda gwamnan jihar Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto ke cewa

“Sojojin Najeriya sun taimaka gaya wajen samar da hadin kai da zaman lafiya a cikin kasar, kuma sun taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a wasu kasashe, a karkashin shiraruwan samar dazaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka da na majalisar dunkin duniya”, saboda haka a cewar sa “'yan mazan jiyan na bin Najeriya bashi da ya kamata a biya”.

To sai dai duk da sanin hakan, kula da tsofaffin sojin, kamar yadda wasu daga cikinsu suka bayyana, bai taka-kara-ya-karya-ba.