Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na AmsoshinTambayoyinku.
Yau za a ji kashi na daya, na amsoshin tambayoyin masu sauraron da dama, game kasar Falasdinu, Isira’ila, Gaza da kuma Hamas. Kamar haka:
1. “Ku bani tarihin kasar Falasdinu da ke zirin gaza. Shin ko akwai mabiya addinin kirista a cikin falasdinawa da ke fafutukar neman yancin kasar su daga kasar isira'ila?” Mai Tambaya: Attahiru Hashimu garin-yerima karamar hukumar Gassol, Taraba, Najeriya.
2. “Ina ne kasar Israila ta ke kafin Isira’ilawa su mamaye kasar Falasdinu? Kuma daga ina ne su Isra’ilawan suka fito?” Mai Tambaya: Malama Mercy Joseph daga Shendam jihar Filato a Najeriya.
3. “ Salam VOA Hausa Zuwa ga Filin amsoshin takardunku. Don Allah Ku bincika min Takaitaccen tarihin Kungiyar Hamas da kuma Tarihin Yankin Zirin Gaza.” Mai Tambaya: Bello Isiyaku Birin Fulani karamar hukumar Nafada jihar Gomben Najeriya.
To idan malamai masu tambaya: Attahiru, da Mercy, da Bello da duk sauran masu sha’awar ji na tare da mu, za a ji kashi na dayan na amsoshin da wakilinmu a shiyyar Adamawa da Taraba, Muhd Salisu Lado, ya samo maku daga Dr. Mahadi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawa Najeriya.
A sha bayani lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5