Yau za a ji kashi na biyu kuma na karshe, na amsoshin tambayoyin masu sauraron da dama, game kasar Falasdinu, Isira’ila, Gaza da kuma Hamas. Kamar haka:
1. “Ku bani tarihin kasar Falasdinu da ke zirin gaza. Shin ko akwai mabiya addinin kirista a cikin falasdinawa da ke fafutukar neman yancin kasar su daga kasar isira'ila?” Mai Tambaya: Attahiru Hashimu garin-yerima karamar hukumar Gassol, Taraba, Najeriya.
2. “Ina ne kasar Israila ta ke kafin Isira’ilawa su mamaye kasar Falasdinu? Kuma daga ina ne su Isra’ilawan suka fito?” Mai Tambaya: Malama Mercy Joseph daga Shendam jihar Filato a Najeriya.
3. “ Salam VOA Hausa Zuwa ga Filin amsoshin takardunku. Don Allah Ku bincika min Takaitaccen tarihin Kungiyar Hamas da kuma Tarihin Yankin Zirin Gaza.” Mai Tambaya: Bello Isiyaku Birin Fulani karamar hukumar Nafada jihar Gomben Najeriya.
To idan malamai masu tambaya: Attahiru, da Mercy, da Bello da duk sauran masu sha’awar ji na tare da mu, za a ji kashi na biyun kuma na karshe na amsoshin da wakilinmu a shiyyar Adamawa da Taraba, Muhd Salisu Lado, ya samo maku daga Dr. Mahadi Abba na Jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, jihar Adamawa Najeriya, wanda ya dan koma baya kadan, ya fara daga fasalin yankin Falasdinu.
A sha bayani lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5