Ghana Za Ta Fara Aiki Da Tsarin Ba Da Biza Bayan An Shiga Kasar

Inda Aka Binne Tsohon Shugaban kasar Ghana Kwame Nkrumah

A wani yunkurin bunkasa harkokin yawon bude ido a Ghana wanda ake so ya zama na daya sannan ya shahara a duniya kamar yadda bangaren Coaco a Ghana ya zama a idon duniya, ministan yawon bude ido, fasaha da al'adu, tare da hadin gwiwar ministan harkokin wajen kasar, da ministan harkokin cikin gida, da hukumar shige da fice ta Ghana, sun amince da shiri ba da biza yayin da ka sauka a Ghana.


Shirin na bayar da bizar bayan shiga Ghana yana cikin wani bangare na shirin shekaru 10 da gwamnati ta aiwatar wato 'Beyond The Return' da nufin karfafa dangantakar 'yan Afirka da ke kasashen waje da samu yin mu'amala da Ghana.

Shirin ba da bizar bayan shigowa Ghana zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Disamban 2023, zuwa 15 ga Janairun 2024.

Mutane suna kalo a wani Barin Wurin da kaka binne marigayi shugaba Kwame Nkrumah.

Malam Hafiz daga ofishin hukumar shige da fice ya ce , za'a bukaci wani daga Ghana ya tsaya wa mai neman biza domin ya shigo ko wanda ya samu takardar gayyata kafin ba da bizar.

Wani mai sana'ar samar da biza ga matafiya Malam Abdul Nasir, Shugaban 'True travel and tour' ya ce ya wannan matakin zai taimaka sosai, kuma zai kawo sauki wajen neman biza, sannan zai taimaka wa kasar Ghana.

Shi kuwa Muhammad Mansur mai son tafiyan yawon bude ido ya ce da sauran kasashen za su kwaikwayi Ghana, da hakan zai taimaka wa masu yawon bude ido.

A saurari rahoton Hawa'u Abdul-Kareem:

Your browser doesn’t support HTML5

Ghana Zata Fara Aiki DaTsarin Bada Biza Bayan Sauka A Kasar (1).mp3