ZAUREN MATASA: Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Sun Hana Shiga Gonakin Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 9 - Oktoba 02, 2023

Nasiru Adamu

Ci gaba da Zauren Matasa a garin Dan Umaru mai yawan jama'a da matasa manoma da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda su ka koka da cewa sun yi yunkurin amfana da damunar bana amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari.

Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samarda abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

A makon jiya mun shiga babi na karshe inda matasan ke baiyana matakin da su ke ganin in an dauka za a samu warware bakin zaren.

Saurari shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

ZAUREN MATASA