Washington, DC —
Rayuwa ba ta gudana kamar yadda ya kamata fa ce sai mutum ya wadatu da bukatunsa na yau da kullum da suka hada da abinci, muhalli, lafiya sutura da dai sauransu. Sai dai kuma tun bayan kullen korona ake fama da tabarbarewar tattalin arziki a fadin duniya. A Najeriya kuwa matsalar ta ninka sakamakon cire tallafin man fetur a bana bayan nadin sabon gwamnati a watan Mayu, wanda aka dade ana kokarin daukan wannan mataki da ya dada ta’azara matsin rayuwar da al’ummar kasar take fama da shi. Mene ne mafita? Aisha Mu'azu ta tattauna da Fatima Muhammad Bature, matashiyar 'yar siyasa kuma 'yar kasuwa da kuma wata daliba, Aisha Danlami Ibrahim.
A saurari cikaken shirin:
Your browser doesn’t support HTML5