AMSOSHIN TAMBAYOYINKU: Me Ya Sa Ake Fama Da Girgizar Kasa A Wasu Kasashe Kawai?

  • Ibrahim Garba

Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalamu alaikum; barkan mu da sake saduwa a wannan shirin na AmsoshinTambayoyinku.

AMBAYA:

Tambayarmu ta yau na cewa, “Wai shin wani dalili ne ya sa a wasu kasashen waje, kamar su Japan da sauran kasashe na yankin Turai, ake yawan fuskantar girgizar kasa, sabanin a wasu kasashenmu na Afurka kamar Najeriya Nijar da Kamaru, inda ba a fuskantar wannan matsalar. Su da suke fuskantar wannan matsalar, me yake janyo musu ita? Mu kuma da ba ma fuskantar ta, mene ne ya sanya haka? Kuma wani mataki ya dace mu dauka don gudun fadawa matsalar.”

MASU TAMBAYA: Sanoussi Madattai Damagaram da Issouhou Makeri Madattai.

AMSA: To idan masu tambayar na saurare, ga kashi na farko na amsar da wakilinmu a Shiyyar Adamawa, Najeriya, Muhammad Salisu Lado, ya samo maku daga Farfesan Jugrafiyya, Abubakar Sadik, na jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, Adamawa Najeriya.

A sha bayani lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

06-03-2023 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU.mp3