Masu ruwa da tsaki a kan man fetur na ci gaba da yin tsokaci game da cire tallafin mai da ya janyo tankiya tsakanin gwamnati da 'yan kwadago
Masu ruwa da tsaki akan harkar man fetur a Nigeria na ci gaba da yin tsokaci akan tirka tirkar da ke tsakanin gwamnatin Nigeria da kuma kungiyar kwadagon game da cire tallafin man fetur,
Tun bayan da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana janye tallafin man ne kungiyar kwadagon ta nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin Najeriya har ma ta yi barazanar tsunduma yajin aiki,
Kwamred Faruk Kawo shugaban Kungiyar Direbobin Dakon Manfetur a Jihar Nejan Nigeriar ya ce a gaskiyar lamari akwai bukatar Kungiyar Kwadagon ta zauna da gwamnati ta yi yarjejeniya mai karfi a kan kudaden tallafin bisa la'akari da yadda hatta wasu manyan hanyoyin Najeriya sun fita hayyacinsu.
Shi kuwa Alhaji Adamu Ahmed Erana, Shugaban kungiyar Dillalan Man Fetur ne a jihar Nejan ya ce duk da yake suna bin gwamnatin Najeriya bashin kudi har sama da naira biliyan 40 amma ba su da wata matsala da cire tallafin domin suna cike da fatan samun sauki nan gaba.
A halin yanzu dai 'yan Najeriya na ci gaba da fama da tashin farashi na kayan masarufi da sufuri jnda har ma a wasu wurare sun ninka har sau biyu.
Saurari rahoton Mustapha Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5