PDP Ta Gargadi INEC Ta Kiyaye Sauya Sakamakon Zaben Jihar Adamawa.

Taron PDP

Majalisar Darektocin Jam'iyar PDP sun ja hankalin Hukumar Zaben Najeriya ta kiyaye sauya sakamakon zaben jihar Adamawa bayan riga-mallam massalacin da wani jami'in Hukumar zabe ya yi

Majalisar amintattun jami’yyar adawa ta PDP tayi wannan bayanin ne da take maida martani akan lamarin da ta ayyana da rashin mutumta dokar kasa da kwamishinan zaben Jihar Adamawa Farfesa Hudu Yunusa-Ari yayi da ya sanar da sakamakon zaben cike gurbin da aka gudanar a jihar.

Kwamishanan zaben ya ayyana ‘yar jam’iyyar APC mai ci Aishatu Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben duk da cewa tana bayan dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamna mai ci a Adamawa Ahmad Fintiri wanda yayi zarra a kananan hukumomi goman da aka bayyana sakamakon kuri’un da aka kada.

Yace ‘yan Najeriya suna fata cewar INEC zata yi adalci a matsayinta na hukumar da bata bangaranci game da zaben cike gurbin da aka gudanar a jihar Adamawa da sauran jihohi a Najeriya.

Kafin a bukaci a sake komawa rumfunan zabe, Fintiri ya baiwa abokiyar karawar tasa rata mai yawa da kuri’u dubu talatin da daya da dari biyu da arba’in da tara (31,249), kamar yadda sakamakon zaben da INEC ta bayyana ya sheda.

Ko da yake INEC a matakin kasa tuni ta soke sakamakon da kwamishinan zaben jihar yayi. Mataimakin shugaban Majalisar kolin mai rikon kwarya Adolphus Wabara, yace rashin mutumta dokar kasa karara, alama ce dake nuni da cewa akwai balagurbi a cikin hukumar INEC.

Ya ce “ bisa la’akari da sarkakiyya da irin jayyayar data dabaibaye zaben ya zuwa yanzu, muna kira ga INEC da ta tabbatar cewa shima wannan zaben bai shiga cikin jerin zabubukan da ake jayyayya akansu ba wanda hukumar ta gudanar”.

Sai dai kuma, shugaban majalisar yayi kira ga ‘yayan jam’iyyar su kasance masu bin doka da oda kuma su kasance masu bin doka da oda cikin natsuwa, kuma su dani cewa, zasu tabbatar cewa marasa da’a da basa mutumta doka basu sace ‘yancin al’ummar Adamawa ba.