KALLABI: Koma Baya Da Mata Suka Samu A Zaben Najeriya, Afrilu, 02, 2023

Shirin Kallabi

Koma bayan da mata suka samu a zaben da aka gudanar a Najeriya na ci gaba da daukar hankalin mata da masu kula da lamura a kasashen nahiyar Afrika da ma duniya baki daya. Wani yanayi da matan suka hanga da ya sa su ka yi ta gangami da fafatukar jan hankalin hukumomi da masu ruwa da tsaki bayanda Majalisar Dattawan Najeriya ta yi fatali da kudurin da zai ba mata kaso talatin da biyar na mukaman gwamnati kamar yadda gwamnatin kasar ta alkawarta.

Banda wannan batun, shirin ya kuma yi hira da Kallabi a fannin wasannin fina-finai da wakoki a Jamhuriyar Nijar, Rashida Alfaharin mawaka, a fannin kiwon lafiya kuma mun haska fitila kan Kaciyar mata.

Saurari cikakken shirin da Grace Alheri Abdu ta gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

KALLABI- Komawa Bayan Da Mata Suka Samu Za Zaben Najeriya