Shirin Kallabi, sabon shirin da muka tsara da nufin haska fitila kan gudummuwar da mata ke badawa a ci gaban al’umma, kalubale da su ke fuskanta a rayuwa, da kuma dumbin damamaki da ke akwai a bangarori dabam dabam da mata da dama ba su san da su ba.
A shirin na farko mun yi nazarin ci gaba ko akasasin haka da aka samu a harkokin damawa da mata a mulki a kasashen Afrika.
Duk da yake hakar mata a kasashe da dama na ganin gwamnatocinsu sun aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma bayan babban taron da mata suka gudanar a Birnin Beijing, a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, na ba mata dama su bada gudummuwa a harkokin siyasa da shugabanci bata cimma ruwa ba, akwai mata bila’adadin da suka yi fice a kowacce fuskar rayuwa, kama daga likitoci, lauyoyi, injiniyoyi, kai har da shugabannin kasashe. Sai dai ba safai ake jin sunayen wadannan kalluba ba, ko yaba irin gudummuwar da su ke badawa. Wannan ne kuma ya sa sau da dama su kan zama ‘yan kallo tsakanin al’umma, duk kuwa da cewa, suna da ilimi da kwarewa kamar mazan da ake ba damamaki.
Rahoton cibiyar nazarin jinsi ta kasa da kasa na baya bayan nan na nuni da cewa, damawa da mata a fagen siyasa, ya yi kasa sosai a Najeriya, abinda ya tabbata a zaben da aka gudanar a matakin kasa da kuma jihohin tarayyar kasar. Inda za mu ka tashi ke nan a wannan shirin Kallabi na farko.
Saurari cikakken shirin da Alheri Grace Abdu ta gabatar:
Your browser doesn’t support HTML5