Rashin kundin dai na da nasaba da sauyin launin kudi da aka yi a Najeriya, lamarin da ya sa har yanzu hada-hadar kudi ta kasa daidaita a kasar kuma a daidai lokacin da aka fara azumin watan Ramadan.
Wannan dai ya zamo wani babban kalubale musamman idan aka yi la’akari da cewa mafi yawan masu kayayyakin da aka fi bukata a cikin watan Ramadan basa tu’ammali da na’urar zamani ta hada-hadar kudi.
A babbar kasuwar Wuse da ke babban birnin tarayya Abuja, wasu ‘yan kasuwa sun ce farashin kayayyaki na hauhawa, don ko a wannan satin shinkafar tuwo da aka saida naira dubu talatin da hudu ta kai dubu talatin da bakwai.
A lokacin azumi dai akan bukaci kayan marmari kamar lemu, mangwaro, kankana, ayaba da sauransu.
Zaharaddin Nuhu, dan kasuwa ne mai saida kayan marmari, ya ce babu abinda ya canza a farashin kayan marmari kuma yana fatan ba za a samu kari ba a farashin.
Wasu ‘yan kasuwa dai sun bayyana tsarin hada-hadar kasuwanci ba tare da musayar tsabar kudi ba a matsayin wani babban ci gaba, yayin da wasu ke ganin hakan na kawo tarnaki ga tsarin kasuwanci.
Sai dai mafi akasari ‘yan kasuwar da ke karkara na kokawa kan sabon tsarin na kasuwanci ba tare da musayar tsabar kudi ba.
Saurari rahoton Hauwa Umar:
Your browser doesn’t support HTML5