Za A Bada Ladan Kamo Maalim Ayman

Maalim Ayman

Amurka za ta bada da tukuici ga duk wanda ke da bayanan da za su kai ga kama ko kuma hukunta 'yan ta'addan da suka kai hari a wani sansanin soja a Kenya shekaru uku da suka wuce.

A ranar 5 ga watan Janairun 2020, mahara talatin zuwa arba'in na bangaren Jaysh Ayman na kungiyar ta'addanci ta al-Shabaab, suka kaddamar da hari a filin jirgin saman soja na Manda Bay a Kenya. Harbe-harben da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi biyo bayan harin sun yi sanadiyar mutuwar sojan Amurka daya da wasu Amurkawa farar hula biyu.

A ranar 5 ga watan Janairu, shekaru uku bayan aukuwar harin, shirn ba da tukuici na Rewards for Justice na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ko RFJ a takaice, ya bayar da tukuicin har zuwa dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama ko kuma a hukunta Maalim Ayman, shugaban sashen Jaysh Ayman na kungiyar al-Shabaab a duk kasar da yake, ko kuma duk wani mutum da ke da hannu a harin, ko ya taimaka wajen kitsa shi, ko goyon bayansa, ko kuma ya taimaka wajen kai harin.

A baya Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya Maalim Ayman a matsayin dan ta'adda na musamman a duniya a karkashin doka mai lamba 13224, wacce aka yi wa garambawul. Haka kuma kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karakshin wani Kwamiti na Somaliya, shi ma ya sanya shi a jerin sunayen 'yan ta'adda.

Idan kai ko wani da ka sani yana da bayani kan ayyuka ko wurin da Malam Ayman yake, ko kuma na wasu da ke da alhakin harin na 2020 kan filin jirgin saman Manda Bay a Kenya, ya tuntuɓi shirin Rewards for Justice ta hanyar kafofin sada zumunta na Signal, ko Telegram, ko WhatsApp a wannan lambar +1-202 -702-7843 a duk duniya, ko kuma a kira +254 71 87 12 366 a Kenya da +252 68 43 43 308 a Somaliya. Duk bayanan da aka samu za a sakayasu. Ana kuma iya samun ƙarin bayani game da wannan tayin tukuicin a shafinn yanar gizo na Rewards for Justice.

Za a binciki duk kwararan rahotannin da aka samu kuma za a bayanin duk wadanda suka ba da bayani zai zam sirri.