‘Yan sanda a jihar Ebonyi sun ce suna gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya haddasa gobarar da ta cinye ofishin hukumar zabe ta kasa da ke karamar hukumar Izzi.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.
Kafafen yada labarai da dama dai sun ruwaito cewar wasu bata-gari ne suka cinna wa ofishin hukumar zaben wuta tare da lalata kimanin akwatin zabe 340 da kuma katin zabe na dindindin da ba a tabbatar da adadinsu ba.
Kakakin hukumar zabe Festus Okoye ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar jiyan, lokacin da wasu da ba a san ko su waye ne ba suka cinna wa ofishin wuta.
“Ban san ko akwai wadanda ake zargin su da aikata wannan ba. Bayanin da nake da shi shine gobatara ce ta cinye wurin. Amma muna nan muna gudanar da bincike, kuma jami’an sashen bincike zasu bayyana da duk abin da zan gaya jama’a.” kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Chris Anyanwu ya shaida wa Sashen Hausa na Muryar Amurka.
“Shin babu jami’an tsaro da ke gadin wurin ne? Ai su ya kamata a tambayi ainihin abin da ya faru, don gano ko gobarar daga lantarki ne ko kuma da gangan ne wasu bata-gari suka cinna wuta. Wannan na bukatar a bincika da kyau. Da yake wannan ma ya faru a wasu jihohin na nuna cewa akwai takun siyasa a cikin al’amarin. Ya kamata a yi bincike da kyau.” In ji Dr. Celestine Nwosu, malami a sashen koyar da kimiyar siyasa a jami’ar jihar Abia.
Najeriya na shirin gudanar da zaben gama-gari a shekara mai zuwa inda za a zabi shugaban kasa, Gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki a matakin jiha da tarayya.
Saurarin cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5