Shekaru 9 Da Sallamar Ma'aikatan PHCN Har Yanzu Babu Batun Hakkinsu

Sarfilu Hashiim Gumel

A sabon shirin za mu duba korafin tsoffin ma’aikatan kamfanin wuta na Najeriya PHCN su dubu 50 da a ka sallama daga aiki a shekara ta 2012, yayin sayar da hannun jarin kamfanin ga ‘yan kasuwa.

Tsoffin ma’aikatan wanda su ka kafa kungiyar bin hakkin su, sun sha yin zanga-zanga da rubuta takardu sau curin masaki ga hukumomin da su ka dace, da su ka hada da, hukumar sayar da hannayen jari BPE amma shiru ka ke ji wai Mallam ya ci shirwa.

Amma fara watsa wannan shiri ya sa kungiyar kare hakkin ma'aikata ta NUEE ta shiga wannan batu, da ya kai ga tafiya yajin aikin da yaso ya jefa Najeriya cikin duhu.

Saurari kashin farko na shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

Shekaru 9 Da Sallamar Ma'aikatan PHCN Har Yanzu Babu Batun Hakkinsu - 11'04"

Saurari Kashi Na Biyu:

Your browser doesn’t support HTML5

Shekaru 9 Da Sallamar Ma'aikatan PHCN Har Yanzu Babu Batun Hakkinsu Kashi Na Biyu - 9'06"

Saurari Kashi Na Uku kuma Na Karshe:

Your browser doesn’t support HTML5

Shekaru 9 Da Sallamar Ma'aikatan PHCN Har Yanzu Babu Batun Hakkinsu Kashi Na Uku - 9'35"