An Raba Tallafin Kayan Sana'a Ga Almajiran Makarantun Allo A Jihar Neja

Almajirai a Maiduguri na karatun allo.

A wani mataki na kokarin shawo kan matsalar yawon barace baracen yara almajiran makarantun allo a yankin arewacin Najeriya, wata kungiyar makarantun tsangaya ta kaddamar da rabon tallafin kayan sana’o’i ga wasu almajirai a jihar Neja da ke Najeriya.

MINNA, NIGERIA - Matsalar yawon bara da kananan yara ke yi ta dade tana ci wa wasu ‘yan yankin arewacin Najeriya tuwo a kwarya.

Kungiyar makarantun tsangaya a jihar Neja da ke Najeriya ta ce tana da yakinin matakin zai yi tasiri sosai wajan shawo kan matsalar yawon bara.

Shugaban kungiyar makarantun allo a jihohin arewa maso tsakiyar Najeriya Ambasada Musa Adamu Hadeja, ya ce kungiyar ta dade da fara tunanin aiwatar da shirin amma sai a wannan karon ne tallafin ya kai ga isa ga wadanda ya kamata ya kai garesu, wato almajiran.

Wannan dai wata Sahihiyar hanya ce ta samun nasarar kawo karshen barar kananan yara da sunan karatun allo, a cewar Shugaban Kungiyar makarantun tsangayar a jihar Neja, Alhaji Gwani Abubakar Sadik.

Sakataren Kungiyar makarantun tsangayar Sani Abdurrahman Dajin, ya ce duk da wannan mataki lamarin na bukatar jajircewa. Su ma almajiran sun yaba da wannan tallafin da aka basu.

Almajirai 80 ne dai aka zakulo daga makarantun allo 40 a kananan hukumomin Bosso, Chanchaga, da kuma Paikoro a masarautar Minna, aka raba musu kayan aikin shushana da kuma akwatinan tallar kayan yari.

Abun fata shi ne sauran sassan arewacin kasar zasu bi sahu wajan daukar irin wannan mataki, da masu sharhi suka bada tabbacin cewa zai taimaka wajan samun nasarar da ake bukata ta wannan fuska.

Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Raba Tallafin Kayan Sana’o’i Ga Almajiran Makarantun Allo A Jihar Neja