Aikawa Da Tallafi Ga Wadanda Su Ke Matukar Bukata A Yemen

The State Department Building is pictured in Washington

Yanayin jin kai a Yemen ya cigaba da kasancewa babban abin damuwa ga Amurka. A matsayinta na daya daga cikin manyan kasashe masu ba da gudummawa ga kasar Yemen, Amurka ta samar da sama da dala biliyan 3.4 na ayyukan jin kai domin rage radadin wahalar da mutanen Yemen suke ciki tun lokacin da aka fara rikicin shekaru shida da suka gabata.

A wani bangare Kuma, Amurka ta sanar kwanan nan cewa, za ta dawo da kudaden tallafi na taimakon jinkai ta hanyar kungiyoyi masu zaman kansu a arewacin Yemen don taimakawa biyan bukatun ‘yan kasar marasa karfi da kuma kara karfafa goyon bayan Amurka da ta dade ta na yi domin taimakon da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa ke bayarwa.

Kasar Amurka na tallafa wa wajen ba da man fetur, abinci, da sauran kayayyakin kasuwanci zuwa Yemen. Koda yake, yin hakan yana bukatar ba wai kawai kayan kasuwanci su wuce cikin sauki ta tashoshin jiragen ruwa ba, har ma da a basu izinin wucewa a duk fadin kasar, gami da yankunan da ke karkashin ikon Houthi.

"Abin takaici, shine mun san cewa Houthis na ci gaba da kawo cikas ga yunkurin, ciki har da karkatar da kudade da ake samu daga shigowa da kayayyaki da niyyar biyan albashin ma'aikatan gwamnati ta hanyar take hakkinsu a karkashin yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani," in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Ned Price. “Sakamakon haka, ma’aikatan gwamnati ba sa karbar albashi don haka ba su da kudin da za su sayi abincin da ake samu. "Karkatar da shigo da mai da Houthin ke yi na daya daga cikin hanyoyin da suke kara tabarbarewar matsalar jinkai ga akasarin mutanen Yemen da ke karkashin ikon da suke da shi."

Amurka za ta yi aiki tare da gwamnatocin Yemen da Saudi Arabiya don nemo hanyar tabbatar da abinci da man fetur, da sauran kayan kasuwanci zuwa kasuwannin Yemen kuma da tabbacin cewa 'yan Houthis ba su kwace su ba don sayarwa a kasuwar bayan fage ko don amfani da su wajen kokarinsu na yaki.

Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suna kira ga bangarorin da su fara tattaunawa karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya. Suna ba da shawara kan lokaci don zaman lafiya, inda za a magance batutuwa kamar tsagaita wuta da samun damar shiga tashoshin jiragen ruwa da warware su cikin sauri kuma lokaci guda idan bangarorin suka himmatu kan aiki dalla-dalla.

Mai magana da yawun Price ya ce, "Ta hanyar yarjejeniya mai dorewa ne kawai za mu yi fatan kawar da mummunan matsalar jin kai a Yemen." Goyon bayan irin wannan yarjejeniya shine daidai taken abin da Wakilin Amurka na Musamman kan Yemen Tim Lenderking yake nema ya yi.