Ana Tuhumar Wata Yar China Da Laifin Karya Akan Bizarta

Masu shigar da kara a nan Amurka sun ce, ofishin jakadancin China da ke birnin San Francisco, ya boye wata mai binciken kimiyya, wacce hukumomin kasar suke zargin ta boye musu alakarta da sojojin China.

Jami’an suna tuhumar Tang Juan wacce ke aiki a sashen bincike na Jami’ar San Francisco, da laifin yin karya akan takardar bizarta a ranar 26 ga watan Yuni.

Takardun kotun da ake tuhumar ‘yar Chinar, sun nuna cewa matar ta yi karya a bukatar da ta mika ta neman biza, inda ta ce ba ta da wata alaka da dakarun kasar ta China da ake kira People’s Liberation Army.

Sai dai daga baya, jami’an da ke binciken manyan laifuka na FBI, sun gano wasu hotunan matar sanye da kayan sojojin China a lokacin da suke bincike a gidanta, hade da wasu bayanai da ke nuna ta taba aiki a wata cibiyar bincike da ke jami’ar kiwon lafiya ta dakarun saman kasar ta China.

Takardun kotun dai sun nuna cewa, Tang ta musanta duk wadannan zarge-zarge da ake mata a lokacin da jami’an FBI suka yi mata tambayoyi a ranar 20 ga watan Yuni.

Bayan kamala yi mata tambayoyin ne, Tang ta tsere ta buya a ofishin jakadancin kasar ta China da ke San Francisco.