Kwamred Mustapha Salihu, wanda shi ne Mataimakin Shugaban jam’iyyar ta kasa, shiyyar arewa maso gabas, ya ce tun da mazabar Oshiomhole a jihar Edo ta dakatar da shi, to duk takardun da ya ke sanya wa hannu haramtattu ne.
Kazalika Salihu ya zargi Oshiomhole da nuna son zuciya wajen zabukan fidda gwani na jam’iyyar da hakan ya janyo wa APC asarar kujerar gwamnan jihar Zamfara, Bayelsa da sauransu.
Duk da Salihu bai amince da cewa rade-radin neman ture Oshiomhole na da nasaba da babban zabe a 2023 ba, ya ce don muradun kare jam’iyyar bayan mulkin Shugaba Buhari, ya na da muhimmanci a sauke Oshiomhole daga kujerarsa.
Yanzu haka dai ‘yan sanda ke gadin hedikwatar APC, kuma bayanai sun nuna cewa an rufe ofishin shugaban jam’iyyar don gudun sauya bayanan takardu.
Zuwa lokacin da Kwamred Mustapha Salihu ya zanta da wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya, an samu labarin Oshiomhole ya daukaka karar bukatar dakatar da aiwatar da umurnin kawar da shi daga mukami har sai an kammala shari’a.
Ga hirar da wakilinmu Nasir Adamu El-hikaya yayi da Kwamred Mustapha a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5