Kungiyar kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa reshen arewacin Najeriya, ta koka akan irin kalubalen da ke kawo cikas a harkar kasuwanci a arewacin kasar.
Kungiyar ta kirawo wani babban taro na mambobinta da ke jihohi 19 da ke arewacin Najeriya, inda ta ce akwai bukatar gwamnatin Nigeriya ta kawo wa ‘yan kasauwar Arewacin kasar dauki.
Alhaji Usman Baba Sa’idu shi ne shugaban wannan kungiya, kuma ya bayyana dalilin kiran wannan taro, inda ya ce makasudin taron shi ne don tattauna matsalolin da ke tsakanin ‘yan kasuwa, Sannan don su mika wa gwamnatin kukarsu na damuwar da su ke da ita.
Su ma ‘yan kasuwan da su ka halarci wannan taron daga sassan arewacin Najeriya, sun nuna korafinsu, kamar Isa Haruna Shu'aibu shi ne shugaban kungiyar reshen jihar Kano, inda ya ce su na fuskantar matsalolin cin zarafi daga jami’an fasa kwabri.
Mai Magana da yawun hukumar ta fasa kwabri, Controller Joseph Atta, ya ce, hukumar ta na aiki bisa ka’ida da doka.
Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka daga Kaduna, Isa Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5