An ci kamfanin bidiyon YouTube na Google tarar dala miliyan dari da saba’in saboda tattara bayanan sirri na yara da kuma yada su ba bisa ka’ida ba.
Hukumar cinikayya ta gwamnatin tarayyar Amurka ta ci kamfanin na google tarar dala miliyan dari da talatin da shida haka kuma kamfanin zai ba jihar New York dala miliyan talatin da hudu na tara akan wasu zarge-zargen makamantan wannan.
Wannan badakalar ita ce mafi girma da aka taba gani wadda ta shafi dokar gwamnatin tarayya ta shekarar aluf dari tara da cisi’in da takwas, wadda ta haramta tattara bayanai akan yara ‘yan kasa da shekaru 13 ba tare da izinin iyayensu ba.
An zargi kamfanin YouTube da farautar bayanan yara ‘yayan mutanen dake kallon shirye-shiryen yara a talabijin ba tare da izinin iyayensu ba, sannan kuma kamfanin yana nuna tallace-tallacen da aka biya shi miliyoyin daloli don nunawa a talabijin ga jama’a masu kallo.
Har ila yau hukuncin da aka yankewa kamfanin Google ya bukaci YouTube ya sake duba tsarin shirye-shiryen da yake watsawa don amfanin yara kanana a talabijin.