Filato: Har Yanzu Ana Rikici Kan Sakamakon Zaben Jos Ta Arewa

Hotunan zaben 2019

Taron masu ruwa da tsaki kan kin amincewa da sakamakon zaben Filato ta Arewa ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.

Biyo bayan kin karbar kuri’u na yankin Kabong da Tudun Wada a zaben Sanata da ‘dan Majalisar Wakilai, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta kira taron masu ruwa da tsaki don gano inda matsalar take, amma suka tashi ba tare da gano bakin zaren ba, lamarin day a sanya har yanzu ba’a bayyana sakamakon zaben ba.
Kwamishinan hukumar zaben a jahar Filato, Malam Halilu Pai ya shaida wa manema labarai cewa suna kan tattaunawa don warware matsalar kafin su sanar da sakamakon zaben.
A cewar daya daga cikin jami'an jam'iyyar PDP, mazabar da ake rikici akanta dake a Jos ta Arewa tana da mutanen da aka yiwa rijista har dubu 92, kuma an kawo kuri'u dubu 31, wanda hakan ya sa mutane ke tambayar tayaya hakan ta faru? Kuma ba a bayyana sakamakon wanda ya samu nasara ba.