Yayinda a yau 15 ga watan november ake cika kwanaki 500 da wasu ‘yan bindiga suka sace mata da yara kanana kimanin 39 a kauyen N’GALEWA dake yankin DIFFA kungiyoyin kare hakkin jama’a sun bayyana damuwa a game da abinda suka kira halin ko in kular da mahukuntan nijer ke nunawa wannan al’amari da suke ganin ya kai matsayin da shugaba MAHAMADU ISUHU da kansa ne ya kamata ya dauki matakin warwarewa.
Wakilin muryar AMURKA a yamai SULE MUMUNI BARMA ya aiko mana karin bayani.
A taron manema labaran da suka kira domin tunawa da wadanan mata da yara 39 na kauyen N’GALEWA shuwagabanin kungiyoyin fafitikar kare hakkin dan adam sun yi tunarwa akan yanayin da wannan al’amari ya faru..KAKA TOUDA MAMADOU GONI kusa ne a kungiyar AEC.
Shugaban kungiyar CONIDE mai kula da kare hakkin yara MOUSSA SIDIKOU dake cikin waNnan gwagwarmaya ta ceton mutanen N’GALEWA na ganin rashin wani hobbasa daga wajen hukumomi tamkar take hakkin yara ne a kasar da saka hannu a yarjejeniyar kasa da kasa..
Kungiyoyin sun bayyana cewa zasu ci gaba da gwagwarmaya ba fasawa har zuwa lokacin da suka tabbatar wadanan mata da yara na N’GALEWA sun koma hannun iyayansu.