Cizon Maciji Na Kashe Mutane Dubu 81 Kowace Shekara A Duniya - WHO

Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO

Kasashe 192 ne suka aminci da sabon kudurin hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO akan karfafa yaki da cizon maciji dake sanadiyar mutuwar mutane dubu 81 kowace shekara a duk fadin duniya

Gwamnatocin a kasashen duniya sun himmatu wajen karfafa yaki da cizon maciji, wadda ya zama wata annobar dake kashe mutane a kalla kusan dubu 81 a kowace shekara.

Wani kudirin hukumar lafiya ta duniya wato WHO,shine ya yunkura wajen inganta wannan yaki da cizon macijin da kuma kare shi tare da samar maganin dafin sa cikin farashi mai rahusa.

Yanzu haka dai kasashen duniya 192 ne suka amince da wannan yunkurin a karshen watan jiya.

Hukumar ta lafiya ta kiyasta majizai masu dafi sun ciji muttane miliyan daya da dubu dari takwas zuwa miliyan biyu da dubu dari 7 a shekara kuma kusan dubu 138 sun mutu.

Hukumar tace sakamakon mutuwar ko wane mutun da maciji ya sara, haka kuma cikin biyar da suka rayu to sau tari hudu daga cikin su zasu kasance da nakasa, musali makancewa, ko yankewar wani gabar jiki ko kuma shanyewar sa, ko kuma zama cikin wani halin rashin sukuni dake da nasaba da gajiya.

Saran maciji dai abu ne da yayi yawa cikin kasashen dake kasashen yamma da sahara, da kudancin asiya da kudu maso gabashin asiya, inji hukumar lafiya ta duniya