Kamfanin General Motors na kasar Amurka, na rokon gwamnatin kasar Amurka ta bashi lasisin kerawa da siyar da mota mai tuka kanta batare da taimakon mutun ba.
Sabuwar motar bata dauke da sikiyari ko giya balle totur, kamfanin dai na sa ran kaddamar da sabuwar motar idan har gwamnati ta aminta da sabon tsarin, za’a fara samar da motar a kasuwa daga shekarar 2019.
Ga mutane kuwa da basu iya bude motar, za’a kayatar da motar da wasu manhajoji da zasu dinga taimakama nakasassu samun saukin sarrafa motar, kamfanin zai inganta motar Chevrolet Bolt EV, za’a kayata motar da tsarin jin Magana da kallo.
Wannan motar zata zama ta farko a cikin jerin motoci masu tuka kansu na haya, kana ta farko maras tsarin matukin kota kwana, kamfanin ya bayyana cewar ta bakin shugaban kamfani Mr. Dan Ammann, a shirye yake ya fitar da motar cikin kasuwa.