Kotun tsarin mulkin Afrika ta kudu ta gano cewar majalisar dokokin kasar ta kasa samun shugaba Jacob Zuma da laifin abun fallasar amfani da miliyoyin dalolin kudaden gwamnati wajen gyara gidan shi.
Wakilin Muryar Amirka a Frika ta kudu Thuso Khumalo ya aiko da rahoto daga birnin Johannesburgv cewa wannan hukuncin zai iya sake bada damar sake yunkurin tsige Jacob Zuma.
Hukuncin ya samu goyon bayan yawancin alkalan kotun tsarin mulki . Alkali Chris Jefta yace majalisar dokokin kasar ta kasa dorawa shugaba Zuma alhakin wannan abun fallasar, kamar yadda dokar ta tanada a sashi na 89 na kundin tsarin mulki, Alhaki Jefta ya kara da cewa majalisa bata da iko ko damar kaddamar da dokar ta sashi na 89.
Sau tara shugaba Zuma ke tsalaka rijiya da baya a yunkurin tsige shi. To amma a yayinda a yanzu jam’iyar ANC wadda take jan ragamar mulkin kasar. take fama da rarabuwar kawuna, masana harkokin siyasar kasar sun yi kashedin cewa da kyar shugaba Zuma ya tsalake yunkurin tsige shi a yanzu.