Gwamnatin Sakkwato Ta Taimakawa Stofaffi a Wani Shirin Gwaji

Gwamnatin jihar Sakkwato ta kaddamar da wani shirin taimakawa tsofaffi marasa galihu da basu da mataimaka da suka hada da maza da dari biyar daga sassa dabam-daban na jihar Sakkwato don saukake musu wahalhalun rayuwa da suke fama dasu.

A cewar shugaban wannan shiri na jarrabawa Malam Lawal Maidoki sakamakon shirin ne zai bada tabbacin makomar shirin a fadin jihar baki daya. Kuma yace hukuma tana sa ran wannan taimako zai rage tsananin talauci da tsofaffi ke fama dasu.

Taimakon zai hada da ciyarwa da tufatarwa da kuma kiwon lafiya musamman cututtukar da tsofaffin ke fama dasu na yawan shekaru. Gwamnatin jihar tace kowane tsoho ya taba taka wata muhimmiyar rawa a ci gaban jihar don haka yakamata a kula da rayuwarsu koda kuwa basu haifu ba.

Wannan shirin gwaji da karkashin hukumar zakka da wakafi na jihar Sakkwato zai kyautata rayuwar tsafaffin da basu da mataimaka, kamar yanda wadansu da suka ci gajiyar wannan shirin suka bayyana, sun nuna farin cikinsu ainun tare da mika dubun godiya ga gwamnati da tayi wannan tunani.

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO GOVT