Sabon dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, wanda tauraronsa ya fara haskakawa a gasar Firimiyar Ingila a bana Alvaro Morata, zai tafi jinya ta tsawon wata guda ko sama da haka.
Wannan ya samo asali ne a sakamakon raunin da ya samu a kafarsa, a wasan da kungiyarsa ta Chelsea tayi da kungiyar Manchester City, a wasan mako na bakwai na gasar cin kofin Firimiya lig na bana ranar Asabar da ta wuce 30/9/2017, inda Manchester City ta bi Chelsea har gida ta doke ta kwallo 1-0.
Alvaro Morata, mai shekaru 24 da haihuwa ya dawo kungiyar Chelsea ne daga tsohuwar kungiyarsa ra Real Madrid, ta kasar Spain. a bana, akan kudi fam miliyan £70 inda ya zamo dan wasa mafi tsada a tarihin kungiyar ta Chelsea.
Ya fafata a wasanni guda bakwai a zuwansa kungiyar Chelsea, ya sami nasarar jefa kwallaye 6 a raga a wasanni daban daban na Firimiyar Ingila ta bana.
Shi dai dan wasan haifaffen dan kasar Spain, ne ya fara taka leda a kungiyar kwallon kafa ta matasa na Getafe, ta Spain, 2008, daga nan ya Koma Real Madrid matasa 2010, 2013.
Ya samu nasarar shiga tawagar babbar kungiyar Real Madrid, a shekara 2014 sai kuma ya tafi kungiyar Juventus, ta kasar itali, a 2014 - 2016 a matsayin aro,
A shekara ta 2016 dan wasan ya dawo kulob dinsa na Real Madrid, inda ya fafata a laliga na kakar wasan 2016/17, inda daga bisani ya dawo kungiyar Chelsea 2017-.
Alvaro Morata ba zai samu damar fafatawa a wasanni da kasarsa Spain zata yi da kasar Albania, da Israel, ba na wasan neman gurbin shiga cin kofin duniya. 2018 ba sakamakon wannan raunin.