Daruruwan mutane ne suka fito kan titunan birnin Barcelona domin yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da fatattakar da ‘yan sanda suka rinka yiwa masu neman ‘yan cin yankin.
Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu ‘dalibai ne sunyi ta ‘daga tutar Catalonia a jiya Litinin, suna kuma ‘daga kwalaye masu rubutu na neman a bari a bi tsarin dimokaradiyya a kofar hedikwatar ‘yan sandan Barcelona. Haka kuma anyi irin wannan zanga-zangar a wasu biranen kasar.
Tashin hankalin dai ya barke ne bayan da ‘yan sanda suka yi yunkurin dakatar da zaben raba gardama da aka shirya yi ranar Lahadi. Jami’an Catalonia sunce kusan mutane 900 ne suka raunata lokacin da ‘yan sanda sukayi kokarin hana mutane kada kuri’unsu, wanda kotu ta ce baya bisa dok
Hotunan bidiyo sun nuna yadda ‘yan sandan suke jan mutane daga wuraren da ake gudanar da zaben, suna dukansu suna bal da su.
Ma’aikatar harakokin cikin gida ta Spain ta fada a jiya Litinin cewa sama da ‘yan sanda 430 da jami’an tsaron farin kaya sun sami raunuka a arangamar da aka yi.
Kungiyar kare ‘yancin bil Adama ta Amnesty International ta ce jami’anta masu lura da lamarin sun shaida cewa ‘yan sandan Spain sunyi amfani da karfi mai yawa akan masu zanga-zangar.