Kashi 2% Cikin 3% Na Amurkawa Na Samun Labaransu Ta Yanar Gizo

A wani sakamakon binciken ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a kasar Amurka, wanda yake nuni da cewar, kimanin kashi 67% na Amurkawa na samun labaran sune daga shafufukan zumunta na yanar gizo ‘social media’

A shekarar 2016, ne mutane da yawan su ya kai kashi 62% na Amurkawa, suka bayyanar da cewar, suna samun labaransu ta wannan hanyar ne, a shafufuka da suka hada da Facebook, twitter, Instagram, da dai makamantan su.

A tsakanin Amurkawa, manya farare, kashi 74%, suna samun labaran su ta yanar gizo ne, wanda aka samu karin kashi 10%, haka mutane da shekarun su ya kai daga 50, sun tabbatar da cewar, suma mafi akasarin labarin da suke samu daga yanar gizo ne.

Hakan na nuni da cewar, shafufukan yanar gizo suna bada gudunmawa wajen yada labarai cikin sauri. Duk dai da cewar shafin facebook suke kangaba a wajen yada labarai a shekarar 2017.

Shafin twitter kuwa na biye da su wajen karas da labarai, da kashi 15%, haka shafin YouTube, suna daga cikin shafufukan da suke da kaso 74% na inda mutane ke samun labaran su a wannan shekarar.