Shahararren kamfanin kera motoci na kasar Germany, “BMW” na kara kaimi wajen fito da motoci masu amfani da wuta, nan da shekarar 2020. Wanda suke kokarin fito da sababbin kira masu launuka daban-daban. Zasu fitar da sababbin tsaruruka goma sha biyu 12.
Sun sanar da hakan ne a ranar Alhamis, wannan wani yunkuri ne na ganin sun shiga gaban kamfanin da suka fara kirkirar mota mai amfani da caji na kasar Amurka ‘Tesla’
Mutane da yawa suna tsoron siyan mota mai amfani da caji, sabo da tsada, da kuma zaman su motoci dake da wuyar gyara. Amma tun bayan fito da sabuwar motar da kamfanin Tesla, su kayi ta ‘Model S’ a shekarar 2012, sai mutane suka fara sakin jiki da sabon tsarin.
Tun daga nan kamfanoni masu kera motoci, ke shiga cikin gasar samar da mota da bata amfani da man fetur ko gas, wanda hakan yake da matukar muhimanci ga lafiyar mutane, wajen rage yawaitar gurbatar yanayi.
A shekarar 2013 ne dai kamfanin na BMW suka kaddamar da sabuwar motar i3, mai amfani da wuta, sunce yanzu a shirye suke su wadatar da motar a ko’ina a fadin duniya. Daga nan zuwa shekarar 2020, motoci masu amfani da wuta zasu kara yawa.
A shekarar 2025 kuwa, zamu fitar da kirar sababbin motoci 12 da babu wada zata dinga amfani da man fetur ko gas, a cewar shugaban kamfanin Mr. Harald Krueger, a wata zantawa da yayi da manema labarai.