A gobe ne Talata idan Allah, ya kai rai ake sa ran shahararren kamfanin wayoyi a duniya Apple, zasu kaddamar da sabuwar wayar su ta ‘iPhone 8’ wadda ake sa rana zata wuce tsara a duniyar kimmiyya da fasahar zamani.
Wayar ta iPhone 8, tana dauke da mashahurin cigaban zamani, da aka inganta wayar, wayar zata zo da wata sabuwar manhaja, wanda wayar zata dinga budewa a yayin da mai wayar ya kalli wayar. A takaice wayar na amfani da yanayin fuskar mutun wajen budewa.
Wannan sabon tsarin ya wuce tsarin da suke da shi a wayar iPnone 7, wadda aka kaddamar da ita shekarar da ta gabata, wadda ake bude ta da taswirar zanen hannu.
Ana ganin cewar dai, babu bukatar fito da sabuwar waya, inda ba’a inganta ta da wasu abubuwan zamani ba.
Don haka yasa wannan wayar ake sa ran zata shiga kasuwa sosai, domin kuwa wayar tana dauke da sabon tsarin cajin waya, batare da makalawa a jikin wutaba, ‘wireless charging’ a turance. Kana wayar tana da saurin da ya kai gudun billiyoyin nisa a cikin dakika daya.
Wakilin DandalinVOA Ibrahim Jarmai, wanda yake babban birnin Silicon Valley, zai cigaba da kawo muna labarai da dimi-dimin su kai tsaye, daga birnin kimmiyya da fasaha na duniya, a jihar California ta kasar Amurka.