A kalla na raini matasan mawaka da furodusa furodusa fiye da hamsin a masana'antar waka cikin tsawon shekaru fiye da ashirin da na shafe ina harkar waka inji mawaki Dauda A Musa, wanda aka fi sani da DarbZ.
Dabz, ya ce ya fara waka ne tun yana dan karami inda yake bin mahaifiyarsa lokacin ta na aiki a matsayinta na malamar asibiti inda ta ke waka don jan hankalin mata kan muhimmancin zuwa asibiti.
Ya kuma kara da cewa yana hip-hop da kuma wakar rauji da ta soyayya, kuma yana wakokinsa a harshen turanci da kuma harshen Hausa.
DarbZ, ya ce bayan waka yana harkar shirya fina-finai kuma yana da kamfanin da yake rainon mawaka tare da daukar faya fayan wakoki.
Babban abinda ke ci wa harkar sa tuwo a kwarya a tabakinsa ya ce bai wuce yadda gwamnati bata baiwa masana'antarsu goyon baya ba.
Your browser doesn’t support HTML5