Kungiyar OPEC ta amince Niger da Libya su hako mai fiye da yadda ta kayade

Ministan mai na Nigeria Emmanuel Ibe Kachikwu a hagu da Sakataren OPEC Abdullah al-Badri.

Shugaban kwamitin dake sa ido ido ga bin ka’idodin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, Issam Almarzooq, ya tabbatarwa kamfanin dilancin labarun kasar Turkiya cewa kungiyar OPEC ta amince kasashen Nigeria da Libya su hako mai fiye da adadin da aka kayadewa sauran kasashen kungiyar

Shugaban kwamitin dake sa ido ido ga bin ka’idodin da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC, wanda kuma shine Ministan mai na kasar Kuwait Issam Almarzooq, ya tabbatarwa kamfanin dilancin labarun kasar Turkiya cewa kungiyar OPEC ta amince kasashen Nigeria da Libya su hako mai fiye da adadin da aka kayadewa sauran kasashen kungiyar.

Kungiyar OPEC ta dauki wannan mataki ne domin daidaita al’amurra a kasuwanin man fetur na duniya.

Tsohon Ministan mai na Nigeria Alhaji Umaru Dembo, ya fadawa wakilin sashen Hausa Hassan Maina Kaina cewa wannan mataki da kungiyar OPEC ta dauka yana nufin cewa kasashen dake cikin kungiyar suna tausayawa junansu ke nan, idan wani abu ya same su.

Yace daga kafa da aka yiwa Nigeria da Libya, gaskiya abu ne na farin ciki da kuma jin dadi domin zai taimakawa kasashen ganin kudin mai yayi kasa. Kudin mai yayi kasa tun ma kafin shugaba Buhari ya dare kan ragamar mulki, kuma daya hau kan mulki farashin mai ya kara faduwa.

Alhaji Umaru yace wannan zai bada bada dama a kara yawan man da za’a hako don saboda a samu karin kudi duk da cewa tsadar shi ba shi da yawa. Idan aka ce sai abinda aka kayyade ne, to kullum ana nan a gidan jiya ke nan a Nigeria da Libya, wadanda yace kowa ya san suna da matsaloli.

Ta fannin tattalin arziki kuma, kwarare irinsu Yusha’u Aliyu na ganin kasashen duniya sun yi la’akari ne da irin halin da Nigeria ke ciki. Yusha’u Aliyu yace kasashen duniya sun fahimci irin halin da Nigeria take ciki da kuma irin gudumawar da take bayarwa wajen tafiyar da kungiyar OPEC da kuma bukatar kasar na samar da mai domin ta samu kudaden shiga wanda zai taimaki tattalin arzikinnta.

Your browser doesn’t support HTML5

OPEC TA AMINCE NIGERIA DA LIBYA SU HAKO MAI FIYE DA YADDA TA KAYADE 3'00